Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Mai magana da yawun Hukumar Peter Afunanya ya yi wannan gargadi, inda yake cewa wadannan fitattun mutane na daga cikin wadanda ke fuskantar barazana daga ‘Yan bindigar da suka addabi jama’ar kasar, musamman ganin cewar akasarin su zasu tafi garuruwan da suka fito domin hutu da kuma ganawa da jama’ar su.
Tuni wasu daga cikin Yan majalisun tarayya suka dinga bayyana damuwar su dangane da tabarbarewar harkokin tsaro a kasar da kuma irin kalubalen da suke fuskanta wajen tafiya garuruwan da suka fito.
Jami’in yayi kuma zargin cewar wasu bata gari na shirin daukar sojojin haya daga daliban da zasu tafi gida hutu domin shiga aikin ‘Yan bindiga da masu garkuwa da mutane da masu fashi da makami da zanga zanga da kuma bijirewa gwamnati.
Jami’in yayi kuma gargadi ‘Yan siyasa da malaman addinai da su shiga taitayin su dangane da irin kalaman da suke yi wadanda yace suna tada hankalin jama’a da kuma tuinzira mutane da ka iy kawo tashin hankali.
342/